HAUSA: HASKEN IDANIYA PART ONE (1)


Part 1
Tafiya yake saman bike dinsa qirar Yamaha, irin wannan katan bike din mummulalle, wanda idan ka na kai sai a ganka kamar ka dan kurkushe yanda shape din bike din ya yi.Ya saka wasu kaya na musamman irinwayanda bike rider suke sakawa. helmet din sa ka dai abar kalloce ba abinda ake gani
a jikinsa komai ya rufe, ya saka wasu hand glove, duka dressing dinsa in black ya yi komai baqi haka bike din nasa ma baki ne……Haka yahau express yana gudu kamar xai tashi sama, bashida damuwar komai a xuciyansa.
 Yana kawowa daidai hotoro kawai sai ga wani saurayi ya bullo shima samannashi bike din amma na farkon yafi girma da alamar tsada.! Suna tafiya su biyu haka sukayi ta bullowa har sukakai su biyar. Amma na farin shi ne kan gaba,da alama shi
ne jagoran su. Yana gaba su kuma su hudun biye da shi a baya.. gudu suke kamar xasu
tada birnin kano.!duk traffic jam din da ake yi a kano da sun shiga xa kuga kamar ana bude musu hanya,in dai ba mutum na san yin asara ba ne. Sannan basa jiran traffic lyt, idan sun danno xakaga suna gudune basa tunanin mixai faru gabansu bare bayan su…
Ganin yanda mutane suke ba su hanya ya tabbatar da cewa su sannannu ne a gari. Basu xame ko inaba sai North-West, tun kafin su qarasa mu ka hango mai gadi ya wangale kofar da sauri ya ja gefe, shigewa ciki suka yi su ka bar mai gadi da qura.
 suka wuce suna xuwa sukayi parking guri daya kamar yanda suke na farkon shine gaba hudun suna bayan sa haka suka yi parking a gu daya. Ganin su samari su ka dau ihu,ana Moh….Moh…. Moh…. Saurayin ne ya daga hannu cikin lalaci irin kamar daga hannun yana mishi wahala, hakan ya tabbatar mana da cewa sunan shine Moh… Wasu kuma naji suna fadin bike riders sun iso…. Lokaci daya suka cire helmet dinsu, ko wanne ya manna katan shade bisa idan sa, mamaki ya cika mu ganin fuskar wannan saurayin da suke kira da Moh.. Ya na da wani abu wait kyau,very handsome,down to earth,ya hadu. & yanada kwarjine da haiba. Gefe guda su ka zauna domin kuwa nan ne wajan zaman su,drinks da su ka bukata aka ka mu su guda hudu kowannan su daya,amma ban da Moh…. Baisha ba,kawai dai ya zauna abun shi yana tauna chewing gum a hankali yana wani hargitsa fuska kamar yaga kashi. Amma hakan da yakeyi da fuska dada fito da kyawunsa yayi.! Kallo daya mu ka ma sa mu ka gane cewa Dan gatane, fuskarsa ma kawai xata nuna maka cewa Dan hutune.!ba tsoro su ka fidda wani dan takarda dauke da wani irin farin gari,suka zuba cikin drinks suka jijjiga,hankali kwance su ke kora shi cikin makoshin su. Suna kare sha, su ka manna helmet dinsu suka hau bike gami da qara wuta… Direct gun bord suka wuce suna zuwa naga duk mutanen gurin sun watse sai wata yarinya wacce iya haduwa ta hadu, da ganin tama irin tanajin kanta saboda kyau da koma komai na ta ya nuna kudi, ita ta ki kaucewa. Suna kawowa naga daya daga chikin su yasa qafa ya shuremata guiwa sai gata a qasa, ya bone kamar ba shine yayi hakanba. kuma ko ajikinsu, Suka qare dube dubensu suka wuce ko kallon ta basuyi ba,tana zaune a gurin ta danne qafa tana kuka… Kai tsaye bike dinsu suka nufa suna shirin fita. Koda suka hangi gate a kulle tun daga nesa suka fara horn amma har suka iso mai gadi bai bude gate ba… Can muka hango mai gadi da gudu yaxo ya bude gate maimakon su fita sai sukayi parking suka sauka gaba dayan su suka nufo shi..Moh ne a gaba suna biye dashi su hudu a baya, Mai gadi yana ganin sun nufo shi ya saki wuta, ya gudu abinshi kada a lallasashi a banza. basuba koni jabo saida nayi dariya but naga khadija sidi batayi dariya ba. Bike riders suka saka dariya gaba dayansu amma Moh…. Wani murmushi kawai yayi da gefen baki, Wanda ya masa kyau. suka hau bike dinsu suka wuce. Maimakon suyi hanyar gida, sai kawai su ka yanki daji, Da Moh ne farko sai lokaci daya su ka tsaya ana daidaitawa, sai kuma qarar bike din ta sauya suka saka wata qara lokaci daya kawai sai naga an fara tsereeee……..

Comments

Popular posts from this blog

GST: Nigerian Peoples and Culture authentic Summary easy to understand for student without stressing yourself